<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><author>Murray, James Ramsey (1841-1905), MacFarland, John T. (1851-1913)</author>
<hymn_number>390</hymn_number>
<title>Can Cikin Baitalahmi, Yesu Ya Zo LW390</title>
<lyrics>[V1]
 1) Can cikin Baitalahmi, Yesu ya zo
 Kamar ɗan jariri Allah ya iso.
 Darajar ta sama ya bar domin mu
 Ya yarda shi zama mutum talaka.

[V2]
 2) Ba gidan mai arziki ko sarauta
 Ba darajar duniya Yesu ya zaɓa
 Ba wurin mafaka domin Ɗan Allah
 Wanda ya yi sama da duk duniya.

[V3]
 3) Ya Yesu Mai Ceto, gareka mun zo,
 Mun kawo yabonmu, Kai ne mu ke so
 Ƙamnar muke ba ka, da godiyarmu,
 Karɓi zukatanmu, ka yi mulkinmu.</lyrics>
</song>